Abokiyar aiki Jummai Ali ta tunbubi Alhaji Ali Kwara wanda ya yi fice dangane da kama 'yan fashi da makami a Najeriya cancanta ko rashin cancantar amincewa da bukatunsu. A nashi ra'ayin bai kamata a baiwa 'yan banga makamai ba domin lokacin da yake kama barayi yawancinsu sun ce sun tuba sun koma garuruwansu sun zama 'yan banga. Ya ce kuma duk garin da aka ce akwai wadannan 'yan bangan akwai rikicin addini da na kabilanci. Wadanda suke da gaskiyar dake cikinsu mafi yawa jahilai ne. Idan dan banga na son ya taimakawa hukuma to ya yi tafiya da soja ko dansanda.
Wasu 'yan bangan 'yan siyasa ne suka kafasu domin neman cin zabe. Alhaji Ali Kwara ya ce akwai wani gwamna da duk 'yan bangansa barayi ne. Sun kashe mutane a koina a kasar. Sai ya koma ya basu albashi. Duk da albashin da ake basu ya ce ya sha kamasu suna fashi. Haka ma a jihar da suke aikin banga suna yiwa gwamnatin sata ana kuma kamasu. Domin haka baiwa 'yan banga bindiga a kasar Najeriya tada hankalin mutane za'a yi, wato za'a saka mutane cikin wani mugun hali na rashin tsaron rayuka da dukiyoyi. Ko suma 'yan sandan ana samun matsala da su.
Idan hukuma ta yi kuskure ta baiwa 'yan banga makamai sata zata karu. Fadace-fadacen kabilanci zasu karu kana a kara samun rikicin addini.Ya ce ko ma basu koma yin sata ba wani gwamna na iya anfani dasu su je su kashe mutane.
Ga karin bayani.