Sojoji da 'yansandan kwantar da tarzoma sune suke shawagi a cikin garin Ibi da kewayensa. Wannan ya biyo bayan kafa dokar hana fita ne ba dare ba rana, sakamakon kashe wasu masu su, da aka yi.
Wani mai magana yace sun shiga wani hali. Yace "abun da ya faru an kashe yaran hausawa su biyu, kana aka raunata daya. Amma kuma da maganar ta shiga gari sai jukunawa suka kashe dayan." Wani ganau yace yan-yanka su aka yi.
Shugaban karamar hukumar Ibin, Isiyaka Adamu ya tabbatar da aukuwar lamarin, kana ya bukaci jama'a da akai zuciya nesa. Yace gwamnati na kokarin shawo kan lamarin. Yace ba fada aka yi ba. Wadanda aka kashe masu, sune kuma 'yan cikin garin Ibi ne. Yace sun je yin sune. Babu wanda ya san wanene ya kashesu, sai dai sun samu labarin cewa an samu gawarwakinsu. Yace yana shirin zuwa wurin da jami'an tsaro sai suka ji cewa 'yanuwan wadanda aka kashe sun tsare wasu da suke zaton sune suka kashe masu 'yanuwa. Yace sai suka yi hanzari suka je wurin suka hana daukar fansa.
Yanzu dai an kara jami'an tsaro domin maido da doka da oda a yankin. Kakakin 'yansandan jihar Taraba Joseph Koje, ya tabbatar da hakan. Ana cigaba da baiwa mutane hakuri, su kai zuciyarsu nesa, su rungumi zaman lafiya yayin da hukumomin jihar ke binciken lamarin.
Ga karin bayani.