Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Fiye da 100 a Zamfara


Wani sojan Najeriya. (File Photo)
Wani sojan Najeriya. (File Photo)
Hukumomin Jihar Zamfara sun ce mutane 119 ne aka kashe a lokacin da wasu 'yan bindiga a kan babura suka kai farmaki kan Unguwar Galadima dake karamar hukumar Maru ta jihar jiya asabar da maraice.

Mutanen garin sun ce wadanda aka kashe sun fi mutane 150. Wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna yace ya kirga gawarwaki 92 a wurin da aka hallara domin yi musu jana'iza yanzun nan. Yace mutanen wasu kauyukan sun riga sun dauki gawarwakin 'yan'uwansu tun jiya a bayan wannan harin.

Haka kuma ana ta shigowa da gwarwakin wasu mutanen da suka mutu a hanya ko a daji.

A kasance da Dandalin VOA domin ci gaba da jin cikakken bayani.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG