Malam Haruna Usman daya daga cikin shugabannin Fulanin kudancin Kaduna yace wata mota ce dauke da Fulani bakwai da hausawa da mafarauta da zasu farauta a wani daji sai sojoji suka tsayarda su suka kama su. Wadanda aka kama sai aka tasa keyarsu zuwa Kafanchan. Ko kafin su isa garin Kafanchan an tseguntawa matasan Kiristoci cewa an kama wasu Fulani 'yan Boko Haram da manya manyan makamai kuma za'a kawo su Kafanachan. Wannan ya sa mutane suka hadu musamman matasa a garin na Kafanchan.
Su matasan Kirista sun yi dafifi a ofishin 'yansanda cewa lallai sai a basu Fulanin su kashesu. Mutane sun yi kokarin kwace makaman sojoji da 'yansanda karfi da yaji lamarin da ya kai ga harbe harbe.
Injiniya Sa'ad Abubakar mazaunin garin Kafanchan ya kara haske kan badakalar. Yace an sa masu dokar hana fita dare da rana. Yace mahukunta suka kama wasu da ake zato Fulani ne da makamai. Sai wasu suka fadawa Kiristoci cewa an kama Fulani da makamai. Jin haka sai suka harzuka suka je ofishin 'yansanda suka yi dafifi da neman a basu Fulanin su kashe. Da aka hanasu sai suka shinge hanyoyi yadda ba za'a iya shiga ko a fita ba. Domin gudun kada wani abu ya faru ya sa mahukunta suka saka dokar.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara.