Gwamnan jihar, Abdulaziz Yari, da mataimakin sifeton janaral na 'yan sanda, Mamman Sule sun samu halartar jana'izar.
Farmakin da yayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dari da ashirin ya faru ne da yammacin Asabar, lokacin da manoma da kungiyoyin 'yan banga daga jihohin Zamfara da Kebbi da Katsina da Kaduna suke wani babban taro a garin na Unguwar Galadima.
Suna taron ne domin samun mafita daga hare-haren da ake kaiwa a yankunasu.
Mutanen da suka abka masu sun zone akan babura, dauke da bindigogi da adduna. Sun harbe wasu, kana kuma sun sassare wasu.
Wani Abdullahi Useini na Unguwar Galadima yace "talakawa ne suka hadu domin kwato 'yancin kansu saboda abubuwan da ake yi masu sun ishesu. Suna cikin taro Allah Ya kawosu. Da suna zaton mutanen taron suka zo, sai da suka ga suna harban mutane, suna murde wa wasu wuya wasu kuma sun fasa kawunansu." A lissafin Abdullahi Useini, an samu rasuwar mutane 155. Akwai wasu da ba'a gansu ba, amma za'a cigaba da nemansu.
A jawabin da gwamnan jihar, Abdulazaiz Yari yayi a wurin jana'izar, ya dora alhakin abunda ya faru akan taron, domin an yi shi ne ba akan ka'ida ba. Yace "idan za'a shirya irin taron dole a nemi izini. Wanda ya shirya taron yana da wani dalili. Gwamnati da jami'an tsaro zasu yi binciken kwakwaf a gano wadanda suka shirya taron har ya kaiga asarar rayuka. Duk wanda aka samu da hannu ciki za'a hukuntasu komai girmansu ko martabarsu." Yace a matsayinsa na gwamnan jihar, babu abun da yasa gaba, illa kare rayukan 'yan jihar da dukiyoyinsu da tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
A 'yan shekarun nan, jihar ta sha fama da hare-hare musamman a yankin gundumar Dansadau, lamarin da yayi sanadiyyar rayukan daruruwan jama'a. Amma wannan harin na ranar Asabar, shi ne mafi muni, wanda ya rutsa da rayuka fiye da dari da hamsin.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.