Mutane da dama aka ce sun rasa rayukansu a wani farmaki da sojoji suka kai kan rugagen Fulani dake Keana jihar Nasarawa. Muhammed Useini sakataren Miyetti Allah reshen jihar Nasarawa ya yi karin haske. Yace jiya da misalin karfe takwas na safe sojoji suka shigo rugagensu da motoci goma da motar sulke daya sai suka soma harbe harbe har da gidan da ake ta'aziya domin rasuwar wani tsoho. Sun kama kashe mutane da jima wasu ciwo. Mata wajenuku aka karye masu hannuwa yanzu suna asibiti. A kidigdigansu mutane talatin da hudu aka kashe.
Muhammed Useini yace kowace kabila da Fulani da wadanda ba Fulani ba ransu ya baci. Yace babu dalilin kawo masu hari. Yace dole a binciki wadanda suka kawo harin kuma ko a kotun duniya sai sun kai karar gwamnatin Najeriya a kan wannan ta'asar da suka yi masu.
Kakakin rundunar 'yansandan jihar Nasarawa Isma'ila Umar ya tabbatar da aukuwar lamarin amma yace kura ta lafa. Yace farmakin da sojojin suka kai bada saninsu ba ne. Yace watakila suna da nasu dalilin. Idan aka samesu kila zasu yi bayani. Yanzu dai 'yansanda na yin kokarin tabbatar da samun kwanciyar hankali.
Garahoton Zainab Babaji.