Shekara daya bayan kaddamar da ayyukan sabuwar Majalisar Dokokin jamhuriyar Nijer ‘yan kasar mazauna kasashen waje sun fara kiraye kirayen ganin an shirya zaben mutanen da za su wakilce su a Majalisar Dokoki, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ta Nijer ya yi tanadi.
A yayin babban baben da Nijer ta gudanar a shekarar 2016 ne ‘yan kasar mazauna kasashen waje suka fara kada kuri’a a kasashen da suke zaune domin aiko da wakilai a Majalisar Dokoki sai dai ba a sami damar gudanar da irin wannan zabe ba a shekarar 2021 sanadiyyar annobar coronavirus, nasarorin da ake ganin an fara samu a yaki da wannan cuta a kasashe da dama, wanda ya sa hukumar zabe ta CENI ta sanar da shirin soma ayyukan rajista a farkon watan Janairun 2022. Sai dai hakan ba ta samu ba, abin da ya haifar da damuwa.
Alhaji Aboubacar Obama dan takara ne a karkashin inuwar jam’iyar MPN kishin kasa daga mazabun yankin Jamhuriyar Benin. Ya jaddada muhimmancin bai wa 'yan Nijer da ke kasashen ketare wannan damar.
Duk da tsaikon da ake fuskanta wajen kaddamar da ayyukan rajistar zabe jagororin ‘yan Nijer da ke kasashen waje na ci gaba da tada magoyansu daga barci kamar yadda sakataren reshen jam’iyar PNDS Tarayya a kasar Belgium, Boubacar Dan Zourmanni, ya bayyana mana.
Daga cikin kujerun wakilci 171 a majalisar Nijer dokokin zabe sun tanadi kujeru 5 domin ‘yan kasar mazauna kasashen waje, rashin aiko da wadannan wakilai kamar yadda ake ciki a yau wani abu ne da ke shafar rayuwar irin wadannan mutane a kasashen da suke zaune.
Shugabannin hukumar zabe sun sha nanata aniyarsu ta shirya ayyukan rajista a kasashen da aka kebe domin bai wa ‘yan Nijer damar morar ‘yancin zabe, to amma a yadda har yanzu wasu kasashe ke dari darin janye matakan yaki da annobar COVID 19 ya haifar da jinkirin da ake fuskanta wajen gudanar da wannan aiki dake bukatar makudan kudade,a yayin da sabuwar majalisar mai wa’adin wakilicin shekaru 5 ke cika shekara 1 da soma ayyukanta.