Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Siyasar Nijar Sun Gargadi Takwarorinsu Na Najeriya Game Da Zaben 2023 Da Ke Tafe 


‘Yan siyasar jamhuriyar Nijer da ke goyon bayan jam'iyya mai mulki da 'yan adawa sun yi kira da ma gargadi ga 'yan siyasar Najeriya game da zabukan gama gari a Najeriya da ke tafe a shekarar 2023.

N’KONNI, NIGER - Yayin da ake shirye shiryen zaben gama gari na shekarar 2023 a Najeriya, takwarorin ‘yan siyasar Najeriya daga jamhuriyar Nijer sun gargadi ‘yan siyasar Najeriya tare da basu shawara akan su yi ingantaccen zabe. Wannan na zuwa ne bayan kammala zaben fidda gwani da jam'iyyun siyasar kasar suka yi.

Alhaji Danbaba Mamman, kakakin jam'iyyar PNDS Tarayya a Birni N'Konni, ya ce su na fata Najeriya za ta yi siyasa mai kawo kwanciyar hankali da lumana duba da yanayin da kasar ke ciki, saboda idan Najeriya ta samu matsala to lallai sauran kasashen yankin ciki har da Nijer zasu fuskanci matsalar.

Su ma ‘yan adawa a Nijer sun yi kira ga ‘yan siyasar Najeriya da su gudanar da yakin neman zabe ba tare da tashin hankali ba ko yin kalamai masu nasaba da addini ko kabilanci da ka iya tayar da husuma, kamar yadda Zubair Sule na jam'iyyar Lumana ya bayyana. Ya kuma yi kira ga 'yan kasar da su maida hankali akan abinda zai kawo musu ci gaba.

Nijer da Najeriya dai makwabtan juna ne, kuma Najeriya ce babbar kasa a nahiyar Afrika ta fannin tattalin arziki, wannan ya sa ‘yan Nijer ke fatan ganin zabukan gama gari da za a yi a 2023 a Najeriya sun samar da maslaha ga matsalolin da kasar da makwabtan ta ke fama da su a halin yanzu.

Saurari cikakken rahoton Harouna Mamane Bako:

‘Yan Siyasar Nijar Sun Gargadi Takwarorinsu Na Najeriya Game Da Zabubukan Kasar Na 2023
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG