Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Bikin Bude Wata Cibiyar Kula Da 'Yan Ta'addan Da Suka Tuba A Jihar Tilabery A Nijar   


Shugaba Bazoum (Facebook/Bazoum Mohamed)
Shugaba Bazoum (Facebook/Bazoum Mohamed)

A Jamhuriyar Nijar an gudanar da bikin damkawa hukumomin kasar wata cibiyar da Majalisar Dinkin Duniya ta gina da hadin gwiwar wasu manyan kasashen duniya cikinsu har da Amurka domin karbar mutanen da suka tuba daga aika-aikar kungiyoyin ta’addancin da suka addabi jama’a a jihar Tilabery.

NIAMEY, NIGER - Rashin aikin yi ko rashin wata kwakwarar madogara na daya daga cikin hujjojin da ake ayyanawa a matsayin dalilan da ke sanya matasa fadawa tarkon kungiyoyin ta’addanci, ko na ‘yan bindiga a irin wannan zamani na yawaitar aika-aika a kasashe matalauta irinsu Nijer.

Hakan ya sa hukumar UNDP da IOM da tallafin kasashe irinsu Amurka suka gina wata cibiya a garin Hamdallaye na jihar Tilabery da nufin karbar mayakan da suka tuba, domin soma yi masu hudubar da za ta taimaka su samu canjin tunani tare da koyar da su sana’oin hucewa kai takaici.

Da yake karbar wannan cibiya a hukunce a madadin gwamnatin Nijar, Ministan cikin gida Hama Souley Adamou ya nuna muhimmancin wannan cibiya ta Centre de Transit.

Wannan cibiya da ke matsayin ta farko da aka kafa a yankin Tilabery mai fama da tashe-tashen hankula wani abu ne da ka iya tasiri wajen samo bakin zaren yanayin da aka shiga yau shekaru fiye da 7.

Mai martaba sarkin Hamdallaye Maiyaki Oumarou Tahirou ya ce yana da kwarin gwiwar cimma burin da aka sa gaba.

Samun irin wannan cibiya a garin Hamdallaye dake matsayin wata mahadar kabilu da al’adu mabambanta wani abin alfahari ne ga baki dayan al’ummar jihar Tilabery.

Wannan ya sa dan majalisar mashawartan da’irar ta Hamdallaye Issouhou Yacouba ke kiran matasa su yi karatun ta nutsu.

A baya, hukumomin Nijar da abokan hulda sun karbi mayakan Boko Haram kusan 400 da suka tuba wadanda aka zaunar a wata cibiyar musamman da ke garin Goudoumaria jihar Diffa don koyar da su ayyuka da sana’oin hannu tare da ba su darussan rayuwa.

Kyawawan sakamakon da aka samu a karkashin wannan yunkuri ya sa kungiyoyin kasa da kasa da manyan kasashen duniya irinsu Amurka suka gina sabuwar cibiya a jihar Tilabery da nufin jan hankulan mayakan kungiyoyin ta’addancin yankin su ajiye makamai don rungumar zaman lafiya.

Saurari rahoto cikin sauti daga Soule Moumini Barma:
An Yi Bukin Bude Wata Cibiyar Kula Da 'Yan Ta'addan Da Suka Tuba A Jihar Tilabery A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00
XS
SM
MD
LG