Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Masu Safarar Miyagun Kwayoyi Suka Koma Bi Ta Kogi Don Tsallakawa Da Hajjarsu A Jamhuriyar Nijar


Wasu daga cikin miyagun kwayoyi da hukumomi suka kwato a hannun masu safarar miyagun kwayoyi, 6 ga watan Satumba, 2022
Wasu daga cikin miyagun kwayoyi da hukumomi suka kwato a hannun masu safarar miyagun kwayoyi, 6 ga watan Satumba, 2022

Kungiyoyin da ke ayyukan waye kan jama’a a game da illolin ta’ammali da miyagun kwayoyi sun bayyana damuwa dangane da yadda al’amarin ke kokarin samun gindin zama a ‘yan shekarun nan a Nijar.

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar gano yadda masu fataucin miyagun kwayoyi suka bullo da dabarar amfani da ruwan kogi don tsallaka iyakokin kasar inda daga bisani masu babura ke isar da hajojin da suka shigo da su zuwa sassa daban-daban na kasar ta Nijar da ma makwabta irin su Libya da Mali.

A yayin da ta ke gabatar da wasu mutanen da ta ce jami’anta sun kama a farkon watan nan na Satumba a birnin Yamai ne, hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi OCRTIS ta sanar cewa masu wannan haramtacciyar sana’a sun fara amfani da hanyar ruwa don kauce wa matakan tsaron kan hanya kamar yadda kakakin hukumar ‘yan sanda ta kasa Commissaire Nana Aichatou Ousman Bako ta tabbatar.

Kungiyoyin da ke ayyukan waye kan jama’a a game da illolin ta’ammali da miyagun kwayoyi sun bayyana damuwa dangane da yadda al’amarin ke kokarin samun gindin zama a ‘yan shekarun nan a Nijar.

Hakan kuwa na faruwa ne duk da matakan da hukumomi ke dauka domin bayanai na nunin dimbin matasa sun rungumi abin ido rufe.

A nata tsokacin, Shugabar kungiyar Emergeance Plus Jamila Amadou na alankata yanayin da aka shiga a yau da sakacin iyaye akan maganar tarbiyyar yara saboda haka ya zama wajibi al’umma ta kula inji ta.

Jamhuriyar Nijar da ke tsakiyar yankin Sahel, na matsayin wata hanyar da masu safarar miyagun kwayoyi da ke fitowa daga kasashen gabar tekun Guinea ke ratsawa a kokarin isar da hajjojinsu zuwa yankin Maghreb.

La’akkari da wannan dabara, ya sa hukumomin kasar tsaurara matakan tsaro dalili kenan su ma dilolin kasa da kasa suka canza salo inda suka fara tsallako kasar ta hanyar Kogin Kwara ko kuma Fleuve Niger, wanda ke ratsa jihohinta 3 wato Tilabery da Yamai da Dosso don cin kasuwannin kasar ko su fita kasashe irinsu Libya da Mali.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:

Yadda Masu Safarar Miyagun Kwayoyi Suka Koma Bi Ta Kogi Don Tsallakawa Da Hajjarsu A Jamhuiryar Nijar - 3'06" .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG