A taron manema labaran da ya kira wanda shine karon farko da ake ganawa tsakaninsa da ‘yan jarida tun bayan da shugaba ISUHU ya bashi mukamin kakakin gwamnati a watan Yunin da ya shige, ministan watsa labaru Abdulrahaman Zakariya ya ja hankula yan jarida akan bukatar su guji rungumar shafukan sada zumunta a matsayin wata kwakwarar majiya domin kaucewa fadawa tarkon masu kokarin kawo yamutsi a kasa..
Rashin samun hadin kan hukumomi a yayin gudanar da bincike domin tantance sahihanci ko gaskiyar wani labari da kuma a wasu lokutan jinkirin da ake fuskanta kafin hukumomi su sanar da jama’a mahimman abubuwan da suka faru a kasa, na daga cikin abubuwan da suke daurewa jita jita gindi a jamhuriyar Niger inji ‘yan jaridar da suka halaci wannan ganawa. To amma sabon kakakin gwamnatin ya ce al’amura zasu sauya daga yanzu.
Editan jaridar LA ROUE DE L HISTOIRE, Ibrahim Moussa wanda ya nuna gamsuwa da sabon tsarin da gwamnatin ke shirin bullo da shi domin karfafawa ‘yan jarida gwuiwa wajen neman sahihan labarai ya ce zasu zuba ido domin su ga kamun ludayin ofishin minista ZAKARIA.
Yawaitar korafe korafen ‘yan jaridar cikin gida akan rashin samun hadin kan hukumomi a yayin neman bayanai da kuma yadda ake samun sanarwar da suka sabawa juna tsakanin jami’an gwamnati a can baya, ya sa shugaban kasar Niger ware ofishi na musamman domin minista ya zama da shi kadai ne ke da hurumin bayarda labaran da suka shafi harakokin gwamnati a hukumance.
A saurari rahoton Souley Mumini Barma
Facebook Forum