A sanarwar da aka aika wa manema labarai mai dauke da sa hannun ministan tsaron Nijer Alkassoum Indatou ma’aikatar tsaron kasar tace wasu ‘yan bindiga dake kan gomman babura da motoci sun yi arangama da jami’an tsaron jandarman kauyen Waraou a wajejen karfe 5 da minti 30 na asubar talata lokacin da suke sinitiri domin tabbatar da tsaro a kauyukan yankin.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa dakarun sun hallaka gwamman 'yan ta'adda tare da jikkata da dama.
An shafe lokaci mai tsawo ana barin wuta a tsakanin jandarmomi da wadanan mahara kafin daga bisani isowar daukin sojan kasa da na saman Nijer har ma da na kasashe aminnai ya bada damar fafatakar su.
Sanarwar tace jandarmomi 8 ne suka rasu sannan wasu 33 sun ji rauni 6 daga cikinsu abin ya yi tsanani wadanda aka kwantar a asibitocin birnin yamai sannan an lalata motocin toyota 5 da babbar motar dakon kaya daya, yayinda ‘yan ta’adda sama da 50 suka sheka lahira sai wasu masu tarin yawa aka jikkata sai dai maharan sun kwashe mutanensu a yayinda suke kokarin arcewa daga inda aka yi wannan kazamin fada.
Ministan yace da sunan shugaban kasa suna jinjinawa asakarawan Nijer saboda jajircewarsu wajen tabbatar da tsaron kasa.
Wannan hari na kauyen Waraou na zuwa kwanaki 3 kacal bayan rangadin da shugaban kasa Mohamed Bazoum ya kai a gudumomin Tera da Gothey dake yankin arewa maso yammacin jihar Tilabery iyaka da kasar Mali, a wannan rana shugaban ya bayyana damuwa game da rashin matakan tsaro kan iyakar Nijer da kasashen Mali da Burkina Faso domin a cewarsa yanayin da ake ciki a wadanan kasashe makwafta ne ke bai wa ‘yan ta’adda damar tsallakowa Nijer hanci sama. Haka kuma ya yi wa ‘yan bindigar da suka addabi yankin Sahel tayin ajiye makamai don rungumar sabuwar rayuwa cikin al’umar da suka fito to sai dai ana ganin harin na jiya talata a matsayin wata amsar daga kungiyoyin dake ikirarin jihadi koda yake kawo yanzu ba kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan farmaki.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: