A taron manema labaran da ya kira ministan Ayyukan Jinkai Alhaji Lawan Magaji ya bayyana cewa ruwan sama ya haddasa barna a dukkan jihohin kasar ta Nijer, koda yake a bana matsalar na da sauki idan aka kwatanta da halin da ake ciki bara warhaka.
Rashin mutunta ka’idar gini da nuna halin ko in kula a kan batun mutunta hakkin makwabtaka na daga cikin manyan dalilan da suka janyo wannan barna. Alhaji Lawan Magaji ya bada alkaluman asarar da ambaliyar ruwan sama ta janyo, ciki har da mutane 42 da suka rasa rayukansu.
Tuni dai gwamnatin ta fara tallafa wa wadanda wannan bala’i ya afka wa da dan abin masarufi inji ministan. Ya ce an rigada an fara bada gudunmuwar kayan abinci da tabarmi da sauran kayan taimako ga mutane dubu saba’in da ambaliyar ta shafa.
Kawo yanzu kashi talatin cikin dari na tallafin da ake bukata ne ya shigo hannun hukumomi sanadiyyar jan kafar da ake fuskanta daga abokan hulda yayin da a yanzu haka kogin Isa ko Niger ke kara batsewar da ke barazana ga mazauna gabarsa, kuma Ma’aikatar Hasashen Yanayi ta yi gargadin cewa akwai yiyuwar samun saukar ruwan sama mai yawa a watan nan na Satumba.
Daga birnin Yamai ga rahoton Souley Moumouni Barma:
Facebook Forum