Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rufe Iyakokin Najeriya Ya Sa Farashin Kayan Masarufi Tsada A Nijar


Tsawon makonni biyu kenan da kasar Nigeriya ta rufe iyakarta da Nijar, ba tare da tayi bayanin dalilan yin hakan ba.

Sanin kowa ne huldar kasuwanci tana da karfi tsakanin kasashen Najeriya da Nijar, domin mafi yawan 'yan kasuwan Nijar na harkar kasuwancin su a Najeriya.

Wannan rufe iyaka, ya sa 'yan kasuwa da jama'ar gari kokawa, domin sanya su cikin halin takura da yayi. Kayan masarufi sun kara kudi, kasuwar ta tsaya cak. .

Magidanta sun bayyana a cewa suna ji a jikin su domin wannan al'amari ya sa su cikin kunci, yayin da kayan cefane suka yi muguwar tsada. Wata 'yar kasuwa mai zuwa Kano tace rabin kasuwancita ya tsaya tun lokacin da aka rufe iyakar, domin yanzu azaune take.

Wannan al'amari ya dagula lissafi ganin yadda komai ya
tsaya a harkar kasuwa, da wasu harakokin rayuwa.

Ga cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG