Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rufe Iyakokin Najeriya Ya Shafi Kasuwancin 'Yan Kasar Mazauna Nijar


Deandra Harris, a cashier at Gold Coast Trading Company — a West African goods market based in the Bronx, New York, says, "If you do not vote, you're kind of just giving your vote away to whomever does."
Deandra Harris, a cashier at Gold Coast Trading Company — a West African goods market based in the Bronx, New York, says, "If you do not vote, you're kind of just giving your vote away to whomever does."

Bayan kwana biyu da gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokin kasar da wasu kasashe makwafta, ‘yan Najeriya mazauna jamhuriyar Nijar sun koka akan abinda suka kira cikas.

A fadan su, wannan mataki ya haddasawa harakokin kasuwancinsu, saboda rashin shigowar kayayyakin da suka yi oda daga gida, yayinda aka fara fuskantar hauhawar farashin ababen masarufi a kasuwanin kasar Nijar.

Shigo da kaya kirar kamfanonin Najeriya domin sayar dasu a kasuwannin Nijar sana’a ce da wasu ‘yan Najeriya suka dogara da ita shekara da shekaru. Sai dai matakin rufe iyakoki da gwamnatin shugaba Buhari ta dauka a tsakiyar watan jiya, ya jefa irin wadanan ‘yan kasuwa cikin zullumi, sakamakon tsayarwar harakoki kamar yadda suka shaida wa wakilin Muryar Amurka lokacin da ya zagaya kasuwar.

Girman matsalar da aka shiga a yau ya sa kungiyar ‘yan Najeriya mazauna Nijar kiran gwamnatin Muhammadu Buhari da ta dubi halin da wadanan ‘yan kasar ke ciki sanadiyar rufe iyakoki.

Bayanai daga yankunan dake makwaftaka kut da kut da jihohin Arewacin Najeriya na nunin farashin ababen masarufi ya tashi sama, saboda haka jami’in kare hakkin jama’a Salissou Amadou na Sauvons Le Niger ke jan hankula don ganin an tausawaya talakka.

Koda yake hukumomin Najeriya na alankata wannan mataki da yunkurin dakile barauniyar hanyar masu fasa kwabri, da masu safarar makamai da myagun kwayoyi, wata majiyar gwamnatin Nijar na cewa ba su yi zaton haka abin zai zo da tsauri ba.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG