Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dage Ganawar Da Aka Shirya yi Tsakanin Jami'an Amurka Da Na Masar


Ofishin shugaban Masar Abdel Fattah al-Sissi ya ce, duk da haka, shugaban zai gana da tawagar ta Amurka yau.

An dage wata ganawa tsakanin babban mai ba shugaban Amurka shawara, Jared Kushner da kusoshin ma’aikatar harkokin wajen Masar, a abinda ake gani nuna rashin jin dadin shawarar da Amurka ta dauka ne na yanke taimakon agajin da take ba kasar ta Masar.

Yakamata ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry ya gana da Kushner da wasu manyan jami’an Amurka yau Laraba, amma sabuwar ajandar abubuwan da minista Shoukry zai yi ta nuna cewa an soke ganawar.

Wannan matakin dake nuna rashin jin dadin Masar na zuwa ne bayan da Amurka ta dauki shawarar yanke agajin kudi da na makamai na kusan dala miliyan 100 zuwa Masar, da kuma jinkirta bada karin kudade kusan dala miliyan 200 don dakarun sojan kasar. Amurka ta dauki matakin ne don maida murtani akan gazawar da Masar tayi wajen mutunta hakkokin bil’adama da kuma kin sassauta tsauraran matakan da gwamnatin kasar ta dauka akan kungiyoyin kasa da masu zaman kansu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG