Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burin Kasashen ECOWAS Na Samun Kudin Bai Daya Ba Zai Cika Ba -Masana


Wasu Shugabannin ECOWAS
Wasu Shugabannin ECOWAS

Wani kwamishanan ECOWAS ko CEDEAO dake magana da harshen Faransanci ya gargadi Shugaban kasar Nijar da ya yi taka tsantsan saboda samun kudin bai daya da kungiyar ta yi burin samu a shekarar 2020 ba zai yiwu ba saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasashen Najeriya da Ghana ikirarin da wasu masana suka ce makircin kasar Faransa ne

Shugaban hukumar zartaswa ta ECOWAS ko CEDEAO ya gayawa manema labarai a Nijar wai domin ya gayawa shugaban kasar Issoufou mahammadou cewa tabarbarewa tattalin arzikin Najeriya da Ghana ya kawo cikas ga shirin fitar da kudin bai daya, wato ECO wanda kasashen ECOWAS din suka kuduri aniyar soma hada hada dasu a shekarar 2020.

Sai dai masanin tattalin arziki Nuhu Muhammadou Arzika na cewa 'Faransa ba zata bari ba da lalama kuma a yi shi. An jima ana batun.....duk lokacin da aka shirya za'a yi za'a kawo wani cikas da zasu kirkiro su sa a hana.... Yau Faransa kwamishan take samu daga kasashe 15 na Afirka da ta rena kuma take buga masu kudi tana karban kwamisho".

Domin sake tattauna wannan batun shugaban hukumar zartaswa na ECOWAS ko CEDEAO ya shawarci shugabannin kungiyar su kira wani taro domin duba yiwuwar fito da wani kudi na bai daya nan da zuwa shekaru bakwai ko goma.

Rilwanu Abdulrahaman masanin doka yace matakin zai ba kasashen Afirka ta tsakiya damar shiga gaban kasashen yammacin Afirka. Yana mai cewa idan har sai sun kai shekaru 7 ko 10 su kammala to su a tasu kungiyar nan da shekaru hudu sun gama zasu soma anfani da kudin bai daya.

Sakamakon yin la'akari da siyasar dake da nasaba da "dan gida da mai gida" masana na cewa burin kasashen ECOWAS ko CEDEAO na fitar da kudin bai daya ba zai cika ba sai an tsinke wata igiyar da suke ganin tana maida hannun agogo baya, wato dogaron wasu kasashe kan Faransa. An ba da misalin shugabannin kasashen Nijar da Ivory Coast da Senegal da wasunsu cewa suna cikin wadanda Faransa za ta yi masu kashedi idan suna son su yi wani abu daban da bata so.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG