Toshe hanyar ruwa da kuma cika gadoji da kayan shara ya haddasa ambaliyar ruwa wadda ta rushe gidaje fiye da 100 da kayan abinci da kuma dabbobi da sauran dukiyoyi. To amma zuwa lokacin harhada rahoton nan babu asarar rayuka.
Wadanda abin ya shafa sun ce sun yi ta fada ma hukumomi cewa gadar da ke wurin ta yi kadan ta yadda idan aka yi ruwa sosai idan mutane su ka zo sai sun jira. Wani mai magana a madadin sauran wadanda abin ya shafa, ya ce akwai lokacin da ma kawo shawarar a kawar da gadar saboda yadda ta ke hana ruwa gudu to amma sai aka ji tsoro.
Tuni hukumomi su ka fara nazarin al’amarin da zummar daukar mataki da kuma sanin irin daukin da za a kai ma mutane. Mataimakin Magajin Garin Shiyya ta biyu a Damagaram, Abdullahi Musa, wanda ya ziyarce wadanda al’amarin ya rutsa da su, ya ce ana kan kididdigar yawan iyalan da abin ya shafa saboda a dau wadataccen mataki.
Ga Tamar Abari da cikakken rahoton:
Facebook Forum