Wasu 'yansanda a Janhuriyar Nijar, wadanda su ka ba da kashi ma wani dalibi yanzu haka su na nan su na gumi saboda sun shiga rigima saboda yiwuwar su shafe shekara guda a garkame.
Wakilinmu a Jahuriyar Nijar, wanda ya turo da rahoton ya ce:
"Wani bidiyon da aka nada a ranar zanga-zangar dalibai ta 10 ga watan Afirilun da ya gabata wanda kuma aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta ya tona asirin wasu ‘yansanda wadanda su ka sa wani dalibi a tsakiya su ka yi ta dibgarsa da kulake su ka kuma tilasta shi ya ambaci kalaman batunci kan kungiyar dalibai ta kasa, al’amarin da ya sa rundunar ‘yansanda dakatar da daliban kafin daga bisani a danka su a hannun mashara’anta.
Yanzu dai alkali ya yanke shawarar garkame wadannan ‘yansandan a gidan yari na tsawon shekara guda, a yayin da ita kuma gwamnatin Janhuriyar Nijar aka ce ta biya dalibin diyyar Sefa (CFA) miliyan 15, matakin da Mataimakin Sakataren Kungiyar Dalibai ta Nijar Tsalha Kaila ya ce ya yi daidai.”
Ga Haruna Dauda da cikakken rahoton:
Facebook Forum