Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau Ake Zaben Shugaban Kasa A Angola


Shugaba Jose Erduardo na kasar Angola zai bar mulkin kasar bayan kusan karni hudu da ya kwashe akan karagar mulki.

A yau Laraba ne masu kada kuri’a a kasar Angola ke zabar sabon shugaban kasa, don maye gurbin dadadden shugaban kasa Jose Eduardo dos Santos, wanda zai sauka daga kan karagar mulkin kasar bayan shekaru 38 akan kujerar.

Ana sa ran Jam’iyyar Dos Santos ta MPLA dake karkashin jagorancin ministan tsaron kasar Joao Lourenco wanda jam’iyyar ta tsaida a matsayin dan takararta, zata sami isassun kuri’un da zata cigaba da kasancewa a kan mulki.

Sai dai duk wanda ya lashe zaben, zai fuskanci matsalolin tattalin arziki a kasar mai arzikin man fetur da ta fuskanci koma baya sakamakon faduwar farashen man fetur.

Jam’iyyar MPLA ce ke mulkin kasar Angola tun daga lokacin da kasar ta sami ‘yancin kanta daga kasar Portugal a shekarar 1975.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG