Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Masu Satar Mutane an Samu Kaya na Fiye da Miliyan 100


Rundunar ‘yan Sandan jihar Oyo, ta kama wasu masu satar mutane da suka sace wani dattijo mai shakaru tamanin a garin Omu Aran dake jihar Kwara, suka karbi Naira miliyan takwas kudin fansa kafin su sake shi.

Haka ma ‘yan Sandan na jihar Oyo, sun kama wasu masu satar motocin inda aka samu bindigogi da dama da kuma manyan motoci na alfarma.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ta Oyo, Alhaji Muhammad Musa Katsina, yace “ Na farko dai wandannan mutane su hudu, Fulani ne daga jihar Kwara, sun eke tadawa mutane hankali da satar mutane, a Azumin da ya gabata wadannan mutane sun je wani kauye a jihar Kwara, suka sace wani dattijo suka karbi kudin fansa.”

Ya ci gaba da cewa sai kuma suka shigo jihar Oyo da niyyar sace wani Sarki, toh a cikin lungun da suke shirin aiwatar da mugun nufin su ne ‘yan sanda suka samu labari sai aka dunguma zuwa cafke su.

An kama motoci da kayayyaki da kudin su ya haura Naira Miliyan dari, an kuma gama wasu masu satar mai da dangar mai guda saba’in da biyar.

Daga bisani Kamishinarn ‘yan Sandan Muhammad Musa Katsina,ya damkawa wai da aka sacewa mota motar sa.

XS
SM
MD
LG