Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Tura Sojojinta Zuwa Kasar Kamaru


Shugaba Barack Obama.
Shugaba Barack Obama.

Shugaba Barack Obama, ne bayyana haka a cikin wata wasika da ya aikewa Majalisar kasar Amurka.

Amurka, zata tura Sojojinta zuwa kasar Kamaru domin sun gudanar da wani aikin liken asiri ta sararin samaniya akan ‘yan kungiyar Boko Haram.

Shugaba Barack Obama, ne bayyana haka a cikin wata wasika da ya aikewa Majalisar kasar Amurka a ya’u Laraba.

'Yan kungiyar ta Boko Haram, na gudanar da harkokin su a arewacin Kamaru daga sansanin su dake Najeriya.

Shugaba Obama ya ce kimanin Sojoji 90, ne suka nufi kasar ta Kamaru a Litinin dina da ta wuce kuma ana sa ran kimani Sojoji 300, ne zasu kasar ta Kamaru.

Kamaru dai tana cikin kasashen hadin gwiwa dake yaki da ‘yan Boko Haram, sauran kasashen sun hada da Niger, Chadi da Benin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG