Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Burtaniya Sun Yi Gargadi Game Da Yiyuwar Kai Harin Ta’addanci A Birnin Abuja


Bayan Wata Barazana Daga ‘Yan Ta’adda 'Yan Sandan Najeriya Sun Karfafa Tsaro A Abuja Tare Da Karin Ma'aikata
Bayan Wata Barazana Daga ‘Yan Ta’adda 'Yan Sandan Najeriya Sun Karfafa Tsaro A Abuja Tare Da Karin Ma'aikata

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce akwai yiwuwar kai Harin ta'addanci a Najeriya, musamman Abuja.

Amurka da Birtaniya a jiya Lahadi sun yi gargadi kan yiwuwar a kai harin ta'addanci a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya, musamman kan gine-ginen gwamnati, wuraren ibada da makarantu, da dai sauransu.

Najeriya dai na yakar masu tayar da kayar baya da sunan addini a yankin arewa maso gabas, amma a watan Yuli kungiyar IS ta dauki alhakin wani samame a wani gidan yari da ke Abuja, wanda ya yi nasarar kubutar da fursunoni kusan 440, lamarin da ya haifar da fargabar cewa 'yan ta’adda masu tayar da kayar baya na kutsowa daga yankunansu.

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce "akwai karuwar kasadar ta'addanci a Najeriya, musamman Abuja" sannan ya kara da cewa manyan kantunan kasuwanci da cibiyoyin tabbatar da doka da kuma kungiyoyin kasa da kasa na daga cikin wuraren da ke fuskantar hadarin.

"Ofishin jakadancin Amurka zai yi takaitaccen aiki har sai illa masha Allahu," in ji ofishin a cikin sanarwar da aka yi wa 'yan kasar a Najeriya.

Gwamnatin Burtaniya ta yi gargadin cewa 'yan kasarta a Najeriya su kasance cikin shiri saboda "karin barazanar hare-haren ta'addanci a Abuja."

"Harin na iya zama na kan mai uwa da wabi sannan ya na iya rutsawa da muradun Yammacin duniya, da kuma wuraren da 'yan yawon bude ido kan ziyarta," a cewarta

Rashin tsaro, wanda al'mari ne da ya wansu a Najeriya, zai zama wata babbar matsala yayin da masu kada kuri'a su ka dunguma zuwa runfunan zabe a watan Fabrairu mai zuwa don zaben sabon Shugaban kasa wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari.

Ba a samu jin ta bakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Nijeria nan take ba.

- Reuters

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG