Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Bada Kyautar Miliyan Biyar Ga Wadda Ya Tsare Tsohon Jami’in Sudan Da Ya Fice Daga Gidan Yari


Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden
Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden

Gwamnatin Amurka ta ce za ta bada kyautar da zata iya kaiwa har   dala miliyan biyar ga duk wanda ya bata bayanin da zai sa a kama  wani tsohon jami’in Sudan da ake nema ruwa a jallo kan zargin laifukan yaki a Dafur da ya tsere daga gidan yari lokacin da yaki ya barke a shekarar da ta gabata.

Kotun Manyan Laifukka ta Duniya ke farautar Ahmed Harun wadda tsohon babban mataimaki ne ga hambararren shugaban gwamnatin mulkin sojan Sudan, Omar al-Bashir, a bisa zargin rawar da ya taka wurin kafa shahararriyar kungiyar mayakan nan ta Janjaweed da tayi kaurin suna wajen kasha kashen gilla a Darfur a shekarar 2000

A watan Afrilu da ya gabata ne Haroun ya bada sanarwar shi da wasu tsoffin jami’in gwamnatin al-Bashir sun arce daga Gidan Yarin Kober kwanaki kadan bayanda da yaki ya barke tsakanin sojin Sudan da sojin rundunar Rapid Support Forces.

Amurka ta ce mayakan Janjaweed ne suka rikide suka koma Rapid Support Forces din da ake zargi da kisan kiyashi akan kabilu da ba larabawa ba a yammacin Sudan

“Samun zaman lafiya na bukatar adalci ga wayanda lamarin ya shaffa da kuma – ga wayanda aka musguna masu a da da yanzu, in ji Mathew Miller, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka.

"Akwai alaka sosai tsakanin musgunawar da aka yi wa al’umma a karkashin mulkin al Bashir ta hannun mutanen da ake zargi irinsu Harun da tashe-tashen hankalin da ake fama da shi yau a Darfur," in ji shi

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya zargi jami’in rundunar Rapid Support Forces da laifukan cin zarafin bil’adama da kisan jinsi da aka yi.

Amurka ta jima tana aiki da Saudiyya domin neman sulhu tsakanin mayakan amma har yanzu ba a cimma nasara ba.

Akalla mutane 13,000 ne suka rasa rayukansu, a cewar wasu kungiyoyi masu zaman kansu, yayinda Majalisar Dinkin Duniya kuma tace akwai wasu mutane miliyan bakwai da suka rasa matsugunarsu.

Tun shekarar 2007 Kotun Majalisar Dinkin Duniya ta ke neman Harun bisa zargin laifukan cin zarafin bil’adama fiye da 20.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG