Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Ce A Shirye Take Ta Taimakawa Nijar Shawo Kan Takunkuman Da Aka Kakaba Mata


Mohammad Mokhber
Mohammad Mokhber

Iran ta fada jiya Laraba cewa, a shirye take ta taimaka wa Jamhuriyar Nijar da aka yi juyin mulki, don shawo kan takunkumin da kasashen duniya suka kakaba mata, a daidai lokacin da Tehran ke kokarin rage maida da ita saniyar ware da aka yi, ta hanyar karfafa alaka da kasashen Afirka.

WASHINGTON, D. C. - Mataimakin shugaban kasar Iran na farko, Mohammad Mokhber, ya ce kasarsa ta yi Allah wadai da takunkumin na rashin Imani, a wata ganawa da Firai Ministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine.

Ya kara da cewa "Babu shakka zamu bayyanawa abokanmu daga Nijar abinda mu ka koya a wannan "

Tun bayan tawayen juyin Musulunci a shekarar 1979 aka kakabawa Iran takunkumi mai tsanani daga kasashen duniya, amma ta samu hanyoyin kaucewa wasu daga cikinsu.

An kakabawa Iran takunkuma kasa da kasa masu tsauri tun bayan juyin-juya hali na Musulunci a shekara ta 1979, amma ta sami hanyoyi fidda kanta daga wadansu.

Har ila yau Tehran na fuskantar matsin takunkuman da Amurka ta kakaba mata tun bayan ficewar da Washington ta yi a shekarar 2018 daga wata muhimmiyar yarjejeniyar nukiliya da ta bai wa Iran sassaucin takunkumi domin dakile ayyukanta na nukiliya.

Kasar Nijar na fuskantar tsauraran takunkumin tattalin arziki da na kudi daga kungiyar kasashen yammacin Afirka bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023 wanda ya hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum.

A cikin taron, Mokhber ya yaba da "nasarar" da kasar da Faransa ta yi wa mulkin mallaka ta yi, na "kafa gwamnati mai cin gashin kanta" a lokacin wannan juyin mulkin.

Kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama a fannoni daban-daban da suka hada da makamashi, kiwon lafiya da kudi.

A watannin baya-bayan nan Iran ta tabbatar da goyon bayanta ga shugabannin da suka kwace mulki ta hanyar juyin mulki a Mali, Burkina Faso da Nijar.

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi a watan Satumba ya yaba da "jajircewar wadannan kasashen na Afirka" wadanda ke fuskantar "manufofin Turai da mulkin mallaka."

Iran, kamar Rasha da Turkiyya, a shirye take ta karfafa tasirinta a nahiyar Afirka, inda take karfafa alaka a kokarinta na rage wariyar launin fata ( see what this means)- maida ta saniyar ware da aka yi, da kuma kawar da tasirin takunkumin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG