Mista Blinken ya jaddada kudirin gwamnatin Amurka kamar yadda Shugaban Amurka Joe Bidden ya bayyana tun farko cewa, kamata ya yi a ce nahiyar Afurka ba tana ciyar da kanta kadai ba, amma har da kasashe a duniya.
Da ya ke tsokaci kan ziyarar Blinken game da bunkasa tattalin arzikin Najeriya da ma Afurka, masanin tattalin arziki da saka jari Dakta Dauda Muhammad Kontagora ya bayyana cewa,
‘’Wannan ziyarar da Sakataren harkokin wajen Amurka Bliken ya kawo a Najeriya, wani daga cikin alfanunsa shi ne, Najeriya ita babbar kasa ce wadda take da kasuwanni, kamfanonin da ke alaka da wadannan kasashe da kuma su kamfanonin Najeriya za su yi amfani da wannan dama su gane irin bukatu da kasashen Amurika su ke da su na huldar kasuwanci’’
Kafin Sakataren harkokin wajen na Amurikan ya tashi zuwa kasar Angola, ya gana da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, inda ya yi alkawarin cewa, gwamnatin Amurka za ta bai wa kasashen yammacin Afirka karin kudi har dala miliyan arba’in da biyar domin yaki da ayyuka irin na ta’addanci kamar yadda tun farko gwamnatin Amurka ta yi alkawari na yaki da ayyukan ta’addanci a nahiyar.
Tun da farko dai Sakataren Harkokin Wajen na Amurka Blinken, ya kaddamar da wata cibiya da ake kira ‘American corner’ a unguwar Lekki da ke birnin Legas, wurin da za a samu muhawara da musayar ra’ayi tsakanin ‘yan Najeriya da kuma Amurkawa domin bunkasa zamantakewa da kuma cigaba na tattalin arziki da kafa mulkin damukradiyya musamman ma dai a tsakanin matasa.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna