Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Birtaniya Sun Kakaba Takunkumi Kan Kungiyar Makasan Masu Sukar Gwamnati Ta Iran


Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken

A ranar ne litinin ne kasashen Amurka da Burtaniya suka sanar da kakaba takunkumi kan wata kungiyar makasan masu sukar gwamnati ta kasar Iran, a cewar Ma'aikatar Baitulmali ta Amurka.

Kungiyar dai na karkashin jagorancin wani mai safarar miyagun kwayoyi dan kasar Iran ne, Naji Ibrahim Sharifi-Zindashti kuma tana aiki ne a bisa umarnin ma'aikatar leken asiri da tsaro ta Iran wato MOIS.

Kungiyar na kai hari kan masu sukar manufofin gwamnati da 'yan adawa na Iran bisa umarnin gwamnatin kasar.

Kungiyar ta Zindashti ta sha kai hare-hare da dama a kan 'yan adawa, 'yan jarida, masu fafutuka, da tsoffin jami'an Iran don rufe bakin masu sukar gwamnatin Iran.

Ayyukan nasu dai sun hada da kashe-kashe, garkuwa da mutane, da ayyukan kutse a Gabas ta Tsakiya, Turai da Arewacin Amurka.

Gwamnatin Iran na amfani da kungiyoyin masu aikata muggan laifuka masu zaman kansu don boye alakar ta da kashe-kashe da sace-sacen mutane.

Karamin sakatare na baitul malin kula mai kula da sashen ayyukan ta'addanci da leken asiri ta kasa da kasa na Amurka, Brian E. Nelson, ya ce "ci gaba da yunkurin far wa masu sukar manufofin gwamnati da Iran ke yi ta hanyar kai hari ga 'yan adawa da masu fafutuka ya nuna matukar rashin aminta da gwamnatin kasar ke da shi da kuma kokarin fadada akidar danniya a cikin Iran da a kasashen duniya."

Haka kuma, ”Amurka, tare da kawayenta na kasa da kasa, kamar su Burtaniya, za su ci gaba da yaki da zaluncin gwamnatin Iran, kuma za su yi amfani da dukkan kayan aikin da ke hannunsu don dakile wannan barazanar, musamman a kasar Amurka," in ji Biran.

Baitul malin Amurka na da izinin daukar matakin martini akan Iran a ƙarƙashin Dokar Zartaswa ta Amurka mai lamba 13553, wacce ta ba da damar sanyawa Iran takunkumi saboda mummunan take haƙƙin ɗan adam da gwamnatin kasar Iran ke yi.

An yiwa kungiyar MOIS sheda a matsayin mai taka rawa wajen take hakkin bil'adama saboda kuntatawar da take yi wa al'ummar Iran tun daga shekara ta 2009 har zuwa yau.

Kazalika, an kuma ayyana kungiyar a matsayin mai tallafawa kungiyoyin ta'addanci irinsu Hamas, Hezbollah da al-Qaida.

Bayan sanarwar ta ranar Litinin, takunkumin ya toshe tare da bayar da rahoton akan duk wasu kadarori da bukatu na mutanen da ke da alaƙa da kungiyar MOIS da a halin yanzu suke cikin Amurka ko kuma ke ƙarƙashin mallaka ko iko da mutanen Amurka ga Ofishin Kula da Kaddarorin Waje.

Baitul malin Amurka ta ce ta dauki matakin nata ne tare da bankado tuhume-tuhumen da ma'aikatar shari'a da hukumar bincike ta tarayyar kasar Amurka suka yi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG