Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Blinken Zuwa Najeriya: Ya Tattauna Kan Batun Yakin Gaza, Matsalar Tsaro, Tattalin Arziki Da Fasaha


Blinken - Tinubu
Blinken - Tinubu

Ziyarar na da nufin karfafa alakar da ke tsakanin Amurka da Najeriya da kuma lalubo damar yin hadin gwiwa a bangarori daban-daban.

A wata ziyara mai cike da tarihi da ya kai Najeriya, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya tattauna da jami’an Najeriya da suka hada da shugaba Bola Tinubu da ministan harkokin wajen kasar.

Tattaunawar manyan jami'an ta tabo batutuwa da dama da suka hada da samar da abinci da noma da magunguna da kuma tsaro a yankin.

Ziyarar na da nufin karfafa alakar da ke tsakanin Amurka da Najeriya da kuma lalubo damar yin hadin gwiwa a bangarori daban-daban.

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa da ya gudana a Abuja, Ministan Harkokin Waje, ya bayyana jin dadinsa da wannan ziyara, inda ya jaddada kyakkyawar tattaunawa kan muhimman batutuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma bangarori daban-daban.

A yayin ganawar, Shugaba Tinubu ya bayyana muradin Najeriya na samun wakilci a kungiyoyin da ke yanke shawara a duniya, kamar G20 da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Najeriya, kasancewar ta kasa mafi yawan al'umma a Afirka da ke da karfin tattalin arziki, na da burin taka rawa sosai wajen tsara manufofin kasa da kasa.

Mai girma Ministan ya jaddada mahimmancin wakilcin Afirka a hukumomi kamar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, inda kudurorin sukan yi tasiri a nahiyar.

Sakatare Blinken ya amince da muhimmancin Najeriya wajen tsara makomar Afirka sannan ya jaddada kudirin Amurka na samar da hadin gwiwa mai inganci.

Ya yabawa shugabancin Najeriya a wasu tsare-tsare da suka hada da ayyukan sauyin yanayi, tsaro a duniya, har ila yau, ya yaba da kokari da yunkurin da Najeriya ke yi wajen ganin ta bunkasa muryar Afirka a Majalisar Dinkin Duniya.

Tattaunawar ta ta'allaka ne kan damar ci gaban tattalin arziki, musamman a fannin fasaha, inda kamfanonin Amurka ke da sha'awar zuba jari.

Sakatare Blinken ya yaba da shirin aikin dijital na Najeriya, ya kuma bayyana kudurin Amurka na tallafawa Najeriya, samar da ayyukan yi, da bunkasa kirkire-kirkire.

Taron manema labaran ya kuma tabo kalubalen da suka hada da magance cin hanci da rashawa da kuma samar da saukin dawo da jari ga kamfanonin kasashen waje. Amurka ta bayyana goyon bayanta ga sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya tare da amincewa da kalubalen da za su iya haifarwa na gajeren lokaci.

Dangane da lafiyar jama'a, Sakatare Blinken ya bayyana irin manyan shirye shirye da zuba jarin da Amurka ke yi a Najeriya, musamman a kan cutar kanjamau, tarin fuka, da na COVID-19.

An kammala taron manema labarai inda Sakatare Blinken yayi jawabi game da rikicin Gaza.

Ya nanata kudurin Amurka kan ka'idojin tabbatar da yankin Gaza da kuma adawa da duk wani sauyi na dindindin ga tsarinta. Sakataren ya jaddada mahimmancin shirye-shiryen mika mulki da kuma magance bukatun jin kai na al'ummar da abin ya shafa.

~ Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG