Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Ba Isra’ila Na’urar Kare Harin Makami Mai Linzami


Na’urar Kariya Ta Terminal High Altitude Area, ko THAAD
Na’urar Kariya Ta Terminal High Altitude Area, ko THAAD

Tsarin makami mai linzamin na’ura ce ta kasa wacce aka kera don kare kariya daga makamai masu linzami kirar ballistic.

Amurka ta kara saka kanta sosai a rikicin Gabas Ta Tsakiya a ranar Lahadi, inda ta sanar da cewa za ta aike da wata sabuwar na’urar kariya ta makami mai linzami zuwa Isra’ila da kuma sojojin Amurka kusan 100 don gudanar da aikinta, karon farko da aka jibge sojojin Amurka a Isira’ila tun bayan harin da Hamas ta kai a bara.

Shugaba Joe Biden ya umarci Sakataran Tsaro Lloyd Austin da ya aika da na’urar kariya ta Terminal High Altitude Area, ko THAAD, da ma’aikatansa zuwa Isra’ila, in ji Sakataran Yada Labaran Pentagon, Maj. Gen. Pat Ryder ya fada a cikin wata sanarwa.

Tsarin makami mai linzamin na’ura ce ta kasa wacce aka kera don kare kariya daga makamai masu linzami kirar ballistic.

Aika na’urar na zuwa ne bayan da Iran ta harba makamai masu linzami sama da 180 a Isra’ila a watan Oktoba bayan harin da Isra’ila ta kai a Beirut ta kashe shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah, inda a yanzu Isira’ila ke shirin kai harin ramuwar gayya kan Tehran.

Lokacin da aka tambaye shi game da shawarar a ranar Lahadi, Biden ya ce kawai ya umarci ma’aikatar tsaro ta Pentagon ta tura na’urar don kare Isra’ila.

Ya ki amsa tambayoyi da aka yi masa daga baya.

Amurka dai ce babbar mai samar da makamai a Isra’ila kuma Ryder ya fada a ciki sanarwar cewa baturin zai “kara inganta tsarin tsaron sararin sama.”

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG