Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Da Isira'ila Ta Kai Ya Kashe Mutane 15 'Yan gida Daya - Masu Aikin Ceto A Gaza


Masu Aikin Ceto Da Mutane Na Ciro Gawarwakin Mutane Da Su Ka Mutu Bayan Wani Harin Isira'ila
Masu Aikin Ceto Da Mutane Na Ciro Gawarwakin Mutane Da Su Ka Mutu Bayan Wani Harin Isira'ila

Hukumar tsaron fararen hula a Gaza ta fada cewa, wani harin da Isira’ila ta kai da sanyin safiyar ranar Asabar ya kashe mutane 15 daga wani iyalan Falasdinawa, da su ka hada da yara tara da mata uku.

An kai harin ne a gidan iyalan Aljah da ke unguwar Al-Zawaida da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda kakakin hukumar tsaron fararen hula Mahmud Bassal ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Sai dai sojojin Isira’ila ba su bayar da wani bayani nan take ba.

“Adadain wadanda su ka mutu sakamakon harin da Isira’ila ta kai kan gidan iyalan Ajlah da ma’ajiyarsu da ke Al-Zawaida ya kai 15,” in ji Bassal.

Bassal ya ba da jerin sunayen wadanda aka kashe da su ka hada da yara tara da mata uku.

Wani ganau ya ce harin ta sama ya faru ne jim kadan bayan tsakiyar daren jiya Juma’a.

“Makaman roka uku ne suka afkawa gidan kai tsaye,” Ahmed Abu al-Ghoul, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, yayin da masu aikin ceto su ka ciro gawarwakin daga cikin baraguzan gidan da ya ruguje.

Ya ce “Akwai yara da mata da yawa a ciki, me su ka yi da su ka cancanci wannan?”

Hotunan gidan talabijin na AFP da ke nuna abin da ya faru bayan harin, wanda aka dauka bayan wayewar gari, ya nuna yadda masu aikin ceto ke neman gawarwaki a karkashin ginin da ya rushe.

Yakin fiye da watanni 10 da aka kwashe ana gwabzawa tsakanin Isira’ila da Hamas ya yi sanadiyar lalata mafi yawan yankunan Gaza.

Yakin ya barke ne bayan da Hamas ta kai wa Isira’ila hari a ranar 7 ga watan Oktoban bara, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 1,198, galibi fararen hula, a cewar alkalumman da kamfanin dillanci labarai na Faransa AFP ya bayar bisa alkaluman hukuma na Isira’ila.

Mayakan sun kuma kama mutane 251 a lokacin harin, inda 111 daga cikin su har yanzu ana garkuwa da su a Gaza, cikin har da 39 da sojojin Isira’ila su ka ce sun mutu.

Sai dai gangamin sojin Isira’ila na ramuwar gayya ya kashe akalla mutane 40,005 a Gaza, a cewar ma’aikatar lafiya ta yankin da ke karkashin ikon Hamas, wanda bai bayar da cikakken bayani kan mutuwar fararen hula da mayakan ba.

AFP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG