Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isira'ila Ta Kashe Mutane 34 A Wani Matsugunin 'Yan Gudun Hijira


Palestinians inspect a school sheltering displaced people after it was hit by an Israeli strike in Nuseirat in the central Gaza Strip, Sept. 11, 2024.
Palestinians inspect a school sheltering displaced people after it was hit by an Israeli strike in Nuseirat in the central Gaza Strip, Sept. 11, 2024.

Hare-haren da Isira'ila ta kai sun kashe a kalla mutane 34, ciki har da mata da kananan yara 19.

Hare-haren da Isira’ila ta kai a Gaza cikin daren Talata zuwa wayewar garin ranar Laraba sun rutsa da wata makarantar Majalisar Dinkin Duniya wadda ta ke zaman matsugunin iyalan Falasdinawa da suka rasa muhallansu da kuma wasu gidaje biyu, sannan, hare-haren sun kashe akalla mutum 34, ciki har da mata da kananan yara 19.

An kai wani mummunan hari da tsakar ranar Laraba, wanda ya rutsa da makarantar Al-Jaouni da ke tsakiyar sansanin ‘yan gudun hijira na al-Nuseirat, inda ya kashe mutum 14 tare da jikkata akalla wasu 18.

Rundunar sojojin Isira’ila ta ce tayi niyyar auna mayakan Hamas da ke shirin kai hare-hare ne daga cikin makarantar.

Daya daga cikin yaran da aka kashe diya ce ga Momin Selmi, mamba a hukumar tsaron farar hula ta Gaza, wadda ke aiki don ceto wadanda suka jikkata da kwaso gawarwaki bayan hare-haren, a cewar hukumar a cikin wata sanarwa.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayi tir da alawadai da harin bom din makarantar. Ya rubuta a wani sakon da ya wallafa a shafin sa na X wanda a baya aka san shi da twitter cewa “Sam abin da yake faruwa a Gaza bai dace ba… Wajibi ne a daina wadannan dabarun take dokokin kare hakkin bil-Adaman.

Akalla ma’aikatan hukumar dake kula da al’amuran ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya UNRWA 220 ne aka kashe tun farkon yakin na Gaza.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG