Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isira’ila Ta Amince Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Yaki Da Hamas


Israel - Netanyahu
Israel - Netanyahu

Wani hadimi ga Firaminista Benjamin Netanyahu ya tabbatar a ranar Lahadi cewa, Isira’ila ta amince da wani tsari na shugaban Amurka Joe Biden don kawo karshen yakin Gaza, ko da yake ya bayyana shi a matsayin mai rauni da ke bukatar karin aiki.

WASHINGTON, D. C. - A wata hira da jaridar Sunday Times ta Biritaniya, Ophir Falk, babban mai ba da shawara kan manufofin kasashen ketare ga Netanyahu, ya ce shawarar Biden "yarjejeniya ce da muka amince da ita amma ba yarjejeniya ba ce mai kyau amma kuma muna matukar son ganin an sako wadanda aka yi garkuwa da su, duk kansu".

Ya ce "akwai bayanai da yawa da za a yi aiki da su." Ya kara da cewa sharuɗɗan Isra'ila da suka haɗa da "sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma rushe Hamas a matsayin ƙungiyar ta'addanci" ba su canza ba.

Biden, wanda ya nuna tsantsar goyon bayan shi ga yakin na Isira’ila, ya samar da kafar kididdigar girman adadin farar hular da su ka mutu, a ranar Juma’a aka nuna abin da ya bayyana da wani tsari mai hawa uku da ta mika gwamnatin Netanyahu da zai kawo karshen yakin.

Kashi na farko ya kunshi yarjejeniyar kawo karshen yakin da kuma dawo da wasu mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su, bayan haka bangarorin za su yi shawarwari kan tsagaita bude wuta a wani mataki na biyu wanda sauran wadanda aka kama za su samu 'yanci, in ji Biden.

Bisa ga dukkan alamu dai jadawalin na nufin cewa, Hamas za ta ci gaba da taka rawa a shirye-shiryen matakan da Masar da Qatar suka samar na shiga tsakani, abun da ka iya cin karo da kudurin Isira'ila na ci gaba da fafutukar kawar da kungiyar Hamas da ke samun goyon bayan Iran.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG