An wayi gari jiya Litini da rikitowar darajar hannayen jari a kasuwannin kasashe, don haka aka ayyana ta da rana mai ban tsoro, lamarin da ya tunatar da duniya mummunan kalubalen tattalin arzikin da ta fuskanta a 1987 da kuma ya afka wa cibiyar hada-hadar kasuwancin ta Wall Street tare da asara mai yawa, yayin da fargaba ke karuwa game da koma bayan tattalin arzikin Amurka.
Kasuwar S&P 500 ta yi kasa da kashi 3%, faduwa mafi muni a wuni a cikin kusan shekaru biyu. Itama kasuwar Dow Jones ta dan yi kasa da 2.6%, yayin da Nasdaq ta yi baya da kashi 3.4% kamar yadda Apple, Nvidia da sauran manyan kamfanonin fasaha da suka kasance taurarin kasuwar hannun jari suka ci gaba da fuskantar nakasu.
Faduwar kasuwannin ita ce ta baya-bayan nan a kalubalen cinikin duniya da aka fara gani a makon da ya gabata. Kasuwar Nikkei ta Japan ta taimaka wa kudin kasar da somawar hada hadar ranar Litinin ta hanyar faduwa da 12.4%, dake zama mafi muni da ta fuskanta cikin wuni tun bayan babbar matsalar tattalin arziki da ake kira da Bakar Litinin a 1987.
Wannan ita ce dama ta farko ga ‘yan kasuwa a Tokyo don daukar mataki biyo bayan rahoton na ranar Juma'a da ke nuna masu daukar ma'aikata a Amurka sun rage daukar ma'aikata a watan da ya gabata fiye da yadda masana tattalin arziki ke tsammani.
Wannan shi ne sabon bayanan da aka samu kan tattalin arzikin Amurka da zai zo da nakasu fiye da yadda aka yi hasashe, kuma ya kara tayar da fargabar cewa baitulmalin Tarayya ya taka wa tattalin arzikin Amurka birki sosai na dogon lokaci ta hanyar kara kudin ruwa da fatan dakile hauhawar farashin kayayyaki.
Dandalin Mu Tattauna