Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: ‘Yan Sanda Sun Yi Nasarar Cafke Wanda Ake Zargi Da Kashe Eunice Dwumfour 


Eunice Dwumfour
Eunice Dwumfour

Bayan kimanin watanni ana bincike, an yi nasarar kama wani da ake zargi da harbin da ya kashe Eunice Dwumfour mai shekaru 30 da haihuwa.

WASHINGTON, D.C. - Dwumfour ta yi nasarar lashe zaben majalisar wakilan birnin Sayreville da ke New Jersey, a Amurka.

Wanda ake zargin ya harbe ta ne yayin da take zaune a cikin motarta a wajen kofar gidanta a ranar 1 ga watan Fabrairu.

Ranar Da Aka Kashe Eunice Dwumfour
Ranar Da Aka Kashe Eunice Dwumfour

Dwumfour ta kasance uwa ga ’ya mai shekara 12, tana kuma taimako da ayyuka a cocinta, kuma ta auri wani Fasto ‘dan Najeriya.

An harbi Dwumfour sau fiye da goma a cikin wannan daren a lokacin sanyi.

Bayanai sun yi nuni da cewa, nan take makwabta suka kira ‘yan sanda, wadanda suka tarar da Dwumfour ta kife a gaban kujerarta cikin motar.

Ranar Da Aka Kashe Eunice Dwumfour
Ranar Da Aka Kashe Eunice Dwumfour

An ga alamar cewa motar tana kunne a lokacin harbin domin motar ta yi tafiya na kusan kafa 100 kafin ta fada kan wasu motoci guda biyu da ke gefen hanya.

Duk da cewa binciken ya dauki watanni amma a karshe, an kama wani wanda ake zargi mai suna Rashid Ali Bynum, ‘dan shekaru 28, daga Portsmouth, jihar Virginia, an kuma tisa keyarshi zuwa gidan yari a ranar Talata 30 ga watan Mayu, inda aka tuhumar shi da Dwumfour.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG