Masana sun ce zai habaka kasuwanci da rage tsadar intanet a Ghana da sauran kasashen Afrika baki daya.
Kamar yadda Ma'aikatar harkokin Kudin Ghana ta yada a shafinta na kafar Tweeter, ta ce “Bayan yarjejeniyar asusun Lamuni na Duniya (IMF), Amurka ta jagoranci hanyar nuna amintuwa da Ghana a matsayin inda za a zuba hannun jari mai riba. Muna maraba da sanarwar zuba jarin dala miliyan 300 daga hukumar ci gaban harkokin kudi (DFC), don gina cibiyar bayanai, irin ta na farko, a Ghana”.
Cibiyoyin Bayanai na Afirka (ADC) na shirin fara aiki kan sabuwar cibiyar da za ta ba da megawatt 10 a karon farko, wanda za iya fadadawa zuwa megawatt 30, a wani fili mai girman kadada 125 dake birnin Accra.
Yakubu Lantam Abdul-Jabar, shugaban kamfanin fasahar zamani, Coldsis, yace, gina wannan cibiyar a Ghana abin murna ne domin cibiyoyin bayanan komfuta da ke kusa, wato Najeriya, Togo da Ghana duk kanana ne, kuma idan Microsoft, Google, Oracle, da AWS na Ingila da suke amfani da su suka dauke, sai sun dangana da Afirka ta kudu. Yace domin haka suna kashe kudi da yawa wajen adana bayanan komfuta da sauran ayyukansu da cibiyar bayanai ke sarrafawa.
Shi ma Musa Inuwa, mai sharhi kan fasahar sadarwar zamani a nasa bangaren ya bayyana muhimmancin cibiyar, idan an kammala ginawa. Yace, “irin taimakon da kasashe maso tasowa, kamar Ghana, ke bukata ke nan” domin cibiyar bayanai zai taimakawa sashen tsaro da kuma tattalin arzikin kasa.
Yakubu Lantam Abdul-Jabar, a nasa bangaren ya kara da cewa, matasa za su samu aikin yi idan wannan cibiyar bayanai ya kammala. Haka kuma zai taimaka wajen kara inganta nau’in fasahar komfuta dake kwaikwayon mutane (Artificial Intelligence), da rage tsadar intanet da ci gaba cikin ayyuka.
Haka kuma, idan an kammala sabuwar cibiyar bayanan, Ghana za ta kasance gurin zuwa ga manyan masu zuba hannun jari da suka dogara da aika bayanan komfuta cikin sauri.
Saurari rahoton Idris Abdallah: