Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Jakadancin Amurka A Najeriya Ya Ce An Gano Jami'ansa Biyu A Raye


Shugaba Amurka Joe Biden, hagu, da takwaran aikinsa na Najeriya Buhari, yayin ziyarar Buhari a Washington (Hoto: Facebook/Femi Adesina)
Shugaba Amurka Joe Biden, hagu, da takwaran aikinsa na Najeriya Buhari, yayin ziyarar Buhari a Washington (Hoto: Facebook/Femi Adesina)

Sanarwar ma'aikatar wajen ta kara da cewa tawagar tana dauke ne da mutum tara 'yan Najeriya inda biyar daga cikin su ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka ne a Najeriya yayin da biyar daga ciki jami'an 'yan sandan kasar ne.

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce an gano jami'ansa biyu a raye wadanda suka bace tun harin da a ka kai kan tawagar su a jihar Anambra a ranar Talatar da ta gabata.

Rahotanni sun ce jami'an suna karkashin kulawar jami'an tsaron Najeriya.

A bayanan ma'aikatar wajen Amurka, ma'aikatan biyu sun bace ne tun ranar Talata bayan wasu mahara da ba a san su waye ba, suka kai farmaki kan tawagar motocinsu a yankin karamar hukumar Ogbaru da ke jihar Anambra a kudu maso gabashin Najeriya.

Sanarwar ma'aikatar wajen ta kara da cewa tawagar tana dauke ne da mutum tara 'yan Najeriya inda biyar daga cikin su ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka ne a Najeriya yayin da biyar daga ciki jami'an 'yan sandan Najeriya ne.

Kazalika tawagar ta yi gaba don sharar fagen ziyarar aiki ta wakilan jakadancin don duba aikin yaki da zaizayar kasa da Amurka ta dauki nauyin aiwatarwa a jihar Anambra.

Maharan sun yi kisan gilla ga akalla 4 daga 'yan tawagar.

A sanarwar ta jiya Jumma'a, ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce wasu wakilansa sun kama hanya don gamuwa da mutanen biyu don raka su zuwa ga iyalansu.

XS
SM
MD
LG