Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun London Ta Samu Ekweremadu, Matarsa Da Laifin Sayen Sashen Jikin Dan Adam


Ike Ekweremadu da matarsa
Ike Ekweremadu da matarsa

Kotun ta saka ranar 5 ga watan Mayun 2023, a matsayin ranar da za a yanke musu hukunci.

Wata kotu a London, ta samu tsohon mataimakin Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu da laifin yunkurin sayen sashin jikin dan adam wanda laifi ne da ya fada ajin bautarwa a zamanance.

Kotun har ila yau ta samu matarsa Beatrice da wani likiti mai suna Dr Obinna Obeta da irin wannan laifi.

An tuhumi iyalan Ekweremadu kan dauko wani matashi dan shekara 21 daga Legas zuwa London don a cire wani sashen jikinsa don a sakawa ‘yar su.

Ekweremadu na da ‘ya mai suna Sonia wacce ke bukatar dashen koda, hakan ya sa suka nemo matashin don ya ba da tashi kodar bisa alkawarin za su biya shi.

Masu shigar da kara a London sun ce su Ekweremadu sun yi wa matashin alkawarin pound dubu 80, inda suka fara ba shi pound dubu bakwai a matsayin kafin alkalami. Sannan sun yi masa alkawarin sama masa aiki mai gwabi.

Sai dai iyalan na Ekweremadu sun musanta wannan zargi.

Kotun dai ba ta ba ta samu ‘yar tasu Sonia mai shekaru 25 da laifi ba bisa tuhume-tuhumen da aka yi wa iyayenta.

Al’amura sun rincabe ne bayan da aka gwada aka ga kodar matashin ba ta yi daidai da ta Sonia ba, hakan ya sa matashin ya tsere ya yi ta gararamba a titinuna London na tsawon kwanaki.

Daga baya sai ya mika kansa wani ofishin ‘yan sanda yana kuka, abin da ya kai ga gudanar da bincike da kama iyalan Ekweremadu.

Bisa doka, ba laifi ba ne ba da koda ga wani da ke bukata, sai dai dokar ta hana ba da kudi a matsayin tukwici.

Kotun ta saka ranar 5 ga watan Mayun 2023, a matsayin ranar da za a yanke musu hukunci.

XS
SM
MD
LG