Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Musanta Mika Malam Gulen Ga Gwamnatin Turkiyya


Shugaba Donald Trump da Shugaba Recep Tayyip Erdogon
Shugaba Donald Trump da Shugaba Recep Tayyip Erdogon

A nan Amurka, fadar White House ta musanta ikirarin da gwamnatin Turkiyya tayi, na cewa shugaba Donald Trump na tunanin mika malamin addinin musulunci nan, Fethullah Gulen ga kasar Turkiyya, malamin da ake nema ruwa-a-jallo.

Wani babban jami’i a fadar White House ya fada a jiya Litinin cewa a yayin da su ka gana da shugaba Erdogan na Turkiyya, a taron kolin G-20 na kasashe masu tattalin arziki da akayi a Buenos Aires na kasar Argentina, shugaba Trump bai ce zai mika Fethullah Gulen ba.

Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya fada a tashar talabijin ta CNBC cewa shugaba Trump, ya fadawa shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, cewa Amurka na shirin mika Gulen tare da wasu mutane ga Turkiyya.

Gulen dai yana gudun hijira ne a jihar Pennsylvania dake nan Amurka, wanda kasar Turkiyya ke zargi da kitsa yi wa Erdogan juyin mulki wanda bai yi nasaraba a shekarar 2016.

Gulen ya musanta wannan zargin, amma Turkiyyar ta bukaci Amurka ta maida mata shi, inda Amurka ta ce Turkiyya ta gaza nuna mata kwararan hujjoji da suka nuna cewa Gulen na da hannu wajen kitsa juyin mulkin.

Cavusoglu yace yaga wani kwakkwaran bincike da hukumar FBI tayi, da ya nuna yadda kungiyar Gulen ke kaucewa biyan haraji a Amurka, shugaba Erdogan ya fada a makon da ya gabata, cewa gwamnatinsa zata fara auna wadanda ke samarwa kungiyar Gulen kudi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG