Babu farar hula a cikin wadanda farmakin ya shafa a kusa da Gandarhse a kusa da gabar tekun kudancin Mogadishu a cewar rundunar Amurka a Afrika.
Dakarun sojin sun ce sun shirya farmakin ne da hadin gwiwar gwamnatin Somalia domin takaita walwalar kaikomon al-Shabab a wurin. A wannan shekara, dakarun Amurka sun kaddamar da farmaki akalla sau 40 a kan manyan tungayen al-Shabab a wurare dabam-dabam a Somalia.
A jiya Asabar kuma wani rikici da zanga-zanga ya shiga kwanaki uku a birnin Baidoa a kan kama Muktar Robow, tsohon mataimakin shugaban al-Shabab kuma babban dan takara a zaben shugaban kasa mai zuwa daga jihar Kudu maso yamma.
Facebook Forum