Zinke shine babban jami’I na biyu da aka bada sanarwar ficewarsu a cikin gwamnatin Trump kasa da wuni guda, kuma wannan ne na baya a cikin jerin jami’ai dake barin gwamnatin bisa zargin aikata almundahana.
A wani sakon Twitter da ya aike a jiya Asabar, Trump yace Ryan ya ci nasara da dama a lokacin aikinsa kuma ina masa godiya da yiwa kasarmu aiki. Ya kuma ce nan da sabon mako zai sanar da wanda zai maye gurbinsa.
Sai dai sanarwar Trump bai bayyana ko Zinke zai yi murabus ko kuma korarsa aka yi, kuma wannan sanarwar na zuwa a lokacin da ma’aikatar shari’a ke nazarin yiwuwar kaddamar da binciken aikata laifi a kansa. Haloli da ayyukansa a ma’aikatar, yasa ana shakku ko yana amfani da matsayinsa domin biyan bukatun kansa, lamarin da ya yi dalilin gudanar da bincike 15 a kansa wanda duka ya tsallake rijiya da baya.
Facebook Forum