Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Faransa Sun Karya Lagon Masu Zanga-Zangar Kasar


'Yan sandan Faransa
'Yan sandan Faransa

Masu zanga-zangar makwanni biyar jere a Faransa sun yi taron gangami a kan tsadar rayuwa a Faransa, koda yake an rinjayi masu zanga-zangar a jiya Asabar a fadin kasar, ta wani bangare saboda bayani da shugaba Emmanuela Macron ya yiwa kasa da kuma ruwan sama da ma yanayin hadari.

Dubban mutane sun halarci taron a babban birnin kasar a jiya Asabar. An samu rigingimu tsakanin masu zanga-zangar da ‘yan sanda da suka yi amfani da barkonon tsohuwa da ruwan zafi a kan masu zanga-zangar yayin da suke maci a kan babban hanyar Champs-Elysees a birnin Paris.

Kimanin ‘yan sanda dubu takwas da motoci masu sulke 14 ne aka jibge domin hana masu zanga-zangar tashin hankali da fasa shagoi suna kwasan kaya da kuma kone-kone da tsare hanyoyi.

‘Yan sandan Faransa sun ce sun kama sama da mutane 115 a jiya Asabar da rana.

A makon da ya gabata, jami’an Faransa sun ce sama da mutane dubu dari ne suka shiga zanga-zangar a fadin kasar. A wannan mako kuma ‘yan sanda sun lissafa mutane dubu 33 ne suka yi zanga-zangar.

Tuni ‘yan sanda suka bude babbar hanyar Champs-Elysees dake Paris da yammacin jiya Asabar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG