Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kammala Zaben Rabin Wa’adi


Amurkawa a rumfar zabe
Amurkawa a rumfar zabe

Amurkawa sun kada kuri'a a zaben rabin wa'adi na farko karkashin shugabancin Joe Biden, inda ake sa ido sosai kan yadda zaben sai tabbar da jam'iyar da ke da iko a Majalisa, kujerun gwamnoni da sauran manyan zabuka.

WASHINGTON, D.C. - Gwamnan Jihar Florida, Ron DeSantis na jam'iyyar Republican ya lashe zaben wa'adi na biyu, inda ya doke dan takarar jam'iyyar Democrat, Charlie Crist, tsohon dan majalisa. DeSantis ya samu nasara a matsayin tauraron Republican na kasa yayin da yake hangen yiwuwar zuwa Fadar White House a 2024.

Gwamnan Jihar Florida Ron Desantis
Gwamnan Jihar Florida Ron Desantis

Sakamakon tseren na majalisar dattijai zai tantance makomar ajandar Biden kuma zai zama kuri'ar raba gardama kan gwamnatinsa yayin da al'ummar kasar ke fama da hauhawar farashin kayayyaki da kuma damuwa kan alkiblar kasar.

Zaben rabin Wa’adi
Zaben rabin Wa’adi
Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden

Da alama ikon Republican na majalisar zai iya haifar da wani zagaye na bincike kan Biden da danginsa, yayin da 'yan jam'iyar Republican a Majalisar Dattijai za su hana Biden nadin masu shari'a.

-AP

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG