Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Asalin Najeriya Da Dama Sun Tsaya Takara A Zaben Amurka


USA-ELECTION/GEORGIA
USA-ELECTION/GEORGIA

An sami karin Amurkawa 'yan asalin Najeriya da suka tsaya takara a zaben wa'adin rabin lokaci da za a gudanar gobe a Amurka.

Daga cikin 'yan kataran, akwai wadanda suke tsayawa takara karon farko a jihohin da ake dauka da muhimmanci a siyasar Amurka.

Carol Kazeem, wata ‘yar asalin Najeriya tana daya daga cikin wadanda suka tsaya takara a zaben rabin wa’adin, wadda ta doke dan majalisa Brian Kirkland a zaben share fage a mazabar lardi ta 159 a jihar Pennsylvania, daya daga cikin jihohin da ake sa ido a zaben.

Nasarar Carol a zaben share fage ya zo da mamaki kasancewa wanda yake rike da kujerar, ya gaje ta ne daga kawunsa a shekara ta 2016, bayan kawun ya rike kujerar na tsawon sama da shekaru 20. Ana kuma daukar iyalin a matsayin jiga-jigan siyasa a mazabar da ba a tunanin wani zai iya kada su a zabe, balle sabon jinin siyasa wadda kuma ta kasance bakar fata ta farko da ta nemi kujerar.

A hirar ta da Muryar Amurka, Carol ta bayyana cewa,

Wannan ce tsayawa ta takara karon farko. A gaskiya yakin neman zaben ya yi wuya ba kamar yadda na zata da farko ba, domin kujerar majalisar jiha na ke nema, kuma mazabar tana da fadi, inda zamu shiga mu yi yakin neman zabe yana da yawa.
Carol Kazeem, 'yar siyasa a jihar Pennsylvania
Carol Kazeem, 'yar siyasa a jihar Pennsylvania

Caron ta ce, da yake wannan ce takararta ta farko, ta fuskanci kalubalen yadda za ta hada kan magoya baya da za su yi mata aiki, da yadda za ta tara kudin yakin neman zabe, da yadda za ta zazzaga ta zaburar da jama’a su fita kada kuria.

Bisa ga cewarta, kasancewarta bakuwa a fannin siyasa ya zama dole ta gabatar da kanta ga masu kada kuri'a domin su fahimci yadda tsarinta ya banbanta.

Tace, "ina takara ne dan takarar da ya shafe sama da shekaru 40 a siyasa, na kuma yi takarar share fage da wanda iyalinsu su ka yi kakagida a siyasar jihar da ake zaton babu wanda zai iya buga kirji ya yi takara da su, na kuma sami nasara na kada su domin mutane sun gaji da gafara sa. Mun gaji da cika baki, bamu ganin ana yiwa al’umma aiki a zahiri. Abinda ya sa na tsaya takara ne nan, sai dai kuma dole in nunawa masu kada kuri’a inda na sa gaba in kuma nunawa masu cewa lallai zan iya."

Segun Adeyina, dan siyasa a jihar Georgia
Segun Adeyina, dan siyasa a jihar Georgia

Da yake tsokaci dangane da jam'iyun da 'yan asalin Afrika su ke tsayawa takara, Segun Adeyina dan takarar majalisar wakilai a jihar Georgia, daya daga cikin ‘yan Najeriya biyar da suka tsaya takarar zuwa majalisar wakilan jihar karkashin tutar jam’iyar Democrat, ya bayyana cewa, yana da kyau a sami wakilci a dukan jam’iyun siyasar kasar.

Ya ce, "Abinda na ke karfafawa, na ke gayawa mutane shine, ba maganar jam’iya ba ce, magana ce ta abinda ya tsone wa al’umma ido. Sabili da haka, muna bukatar wakilci a kowanne bangare. Bai kamata a ce domin ina bakin fata, ni dan jam’iyar Democrat ba ne, ko kuma ni dan Jam’iyar Republican ne domin ni bature ne ba. kamar yadda aka cika ganin mutane suna dauka, amma a karshe duka, magana ce ta abinda ya ke sosawa al’umma rai ,domin a kowanne mataki, ko kuma matsayi aka zabe ka, kana wakilcin al’umma ne."

Iro Omere, 'Yar siyasa a Dallas, Texas
Iro Omere, 'Yar siyasa a Dallas, Texas

rawar-da-mata-ke-takawa-a-zaben-amurka

tasirin-yan-ci-rani-a-zaben-amurka-

dan-asalin-kasar-ghana-ya-zama-dan-majalisa-mafi-karanci-shekaru-a-maryland

yar-najeriya-ta-zama-yar-majalisa-a-amurka

Ita kuwa Iro Omeri, wata matashiya da ke takarar majalisa a birnin Dallas ta bayyana cewa, lokaci ya yi da mata za su shiga siyasa su bada gudummuwarsu ga ci gaban al’umma da kuma ganin an sami inganci a bangarorin da ke daukar hankulansu.

"Tilas ne mu fita mu wakilci kanmu. A lokacin da muke ganin mutane ba su sauraronmu, ko ana watsi da bukatunmu, idan muka ga haka na faruwa, dalilin shi ne domin babu mata da yawa a wuraren da ake yanke shawarwari. Tilas ne mu nemi hanyar shiga wadannan wurare domin a dama da mu."

Banda ‘yan Najeriya, akwai ‘yan asalin kasashen Afrika da dama da suka tsaya takara a zaben rabin wa’adin da za a gudanar gobe a duk fadin Amurka, zaben da ke da muhammanci a siyasar kasa, inda ake nuna kwarjinin ko akasin haka na jam’iyun siyasar kasar ta wajen yawan kujerun Majalisar tarayyar kasar da zasu lashe a zaben.

Yanzu haka dai hankali ya karkara kan zaben jihohi shida da ake dauka a matsayin mafiya muhimmanci a zaben, da suka hada da jihohin Arizona, Geogia, Michigan, Nevada, Pennsylvania, da kuma Wisconsin.

Saurari rahoton cikin sauti:

'Yan Asalin Najeriya Da Dama Sun Tsaya Takara A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG