Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Janye Daga Tattaunawa Da Taliban


Shugaba Trump
Shugaba Trump

A jiya Lahadi Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, ya ce Shugaban Amurka, Donald Trump, a ta bakinsa, "ya yanke shawara madaidaiciya," da ya soke tattaunawar zaman lafiya da shugabannin kungiyar Taliban a makebarsa ta Shugaban kasa.

Shugaban na Amurka ya yanke wannan shawara ne saboda ci gaba da kai hare hare da kungiyar ‘yan ta’addan ta ke yi a cikin kasar Afghanistan.

“Mu na so mu ga sun iya cika alkawuransu” na kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar da yaki ya daidaita kafin a “Saka musu” da ganawa da Trump," abin da Pompeo ya fada kenan a gidan talabijin na CNN. Sai dai bai bayar da tabbacin ko za a dawo da tattaunawar ko lokacin da za a yi ba.

Babban jami’in diflomasiyyar Amurka din ya ce Trump ya shirya ganawar jiya Lahadi a makebarsa ta Camp David da ke wajen birnin Washington da kungiyar Taliban da kuma Shugaban Afghanistan, Ashraf Ghani, ko da yake dama daban daban za a yi ganawar, wadda aka shirya bisa imanin cewa hakan zai "kare muradun Amurka” don kawo karshen ayyukan da Amurka ta shafe shekaru sha takwas ta na yi a Afghanistan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG