Da yake jawabi a wani taro da aka yi a wurin adana litattafai na shugaba Ronald Reagan jiya Lahadi, inda Amurkawa ‘yan asalin Iran suka cika makil, Pompeo ya ce gwamnatin Trump ba za ta yi shiru ba akan abin da ya kira “aikata manyan laifuffuka da keta hakkokin jama’a da gwamnatin Iran ta yi.
Ciki har da danne hakkin al'umma domin biyan bukatar shugabannin, Pompeo ya ce jami’an gwamnati dake manyan mukamai sun wawure dukiyar jama’a ta ayyukan ta’addanci, da kwace, da kuma kokarin yada tsagerancin zuwa wasu kasashen.
Pompeo ya ce muna da hakkin hurawa gwamnatin Iran wuta akan yadda take iya samar da kudade da kuma kaisu wasu wurare, kuma za mu yi haka. A wannan kokarin da mu ke yi, akwai batun sake sanya takunkumi akan harkokin bankin Iran, da kuma fannin makashin kasar. "Kamar yadda muka yi maku bayani a ‘yan makonnin da suka gabata, abinda muke maida hankali akai shine yin aiki da kasashen dake sayen man Iran, ta yadda zasu kusan daina sayen man daga na zuwa 4 ga watan Nowamba" a cewar Pompeo.
Facebook Forum