Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Gayyaci Putin Zuwa Amurka


Shugaba Trump tare Shugaban Rasha Vladimir Putina lokacin da suka gana a Helsinki a ranar 16 ga watan Yuli.
Shugaba Trump tare Shugaban Rasha Vladimir Putina lokacin da suka gana a Helsinki a ranar 16 ga watan Yuli.

Ana kan tattaunawa tsakanin Amurka da Russia dangane da wani taron koli na biyu da za a yi a tsakanin Shugaba Trump da takwaran aikinsa Putin, a cewar Sakatariyar yada labarai ta Fadar white House, Sarah Huckabee Sanders.

Sanders wacce ta bayyana hakan a shafin sada zumunta a jiya Alhamis, ta ce shugaba Trump, ya nemi Mai ba shi shawara kan harkar tsaro na Kasa, John Bolton, da ya gayyaci Putin zuwa Wasington nan da lokacin hunturu, kuma tuni har tattaunawar ta yi nisa.


A lokacin da aka sanar da Darektan tattara bayanan sirri na kasa Dan Coats a wani taro a Colorado, kan batun zuwan Putin nan da wasu watanni, sai ya ce “za su yi dubi kan hadarin da za a iya fuskanta a fannin tattara bayanan sirri, za kuma su sanar da shugaba Trump.”


Sanarwar yiwuwar sake haduwar shugabannin biyun, na zuwa ne kwanaki uku, bayan haduwar da suka yi a Helsinki, taron da ya haifar da suka daga manyan jam’iyun Amurka biyu, saboda Trump ya goyi bayan Putin kan matsayar da ya dauka cewa Rasha ba ta yi katsalandan a zaben Amurka na 2016 ba, domin tallafawa Trump ya samu nasara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG