Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo, jiya Jumma'a, ya jaddada cewa dole ne al'ummar duniya ta matsa lamba ma Koriya Ta Arewa, muddun dai ana so ta kawo karshen shirinta na nukiliya.
"Aiwatar da tsauraran takunkumai wajibi ne ga cimma wannan buri na mu," abin da Pompeo ya gaya wa manema labarai kenan bayan jerin wasu tarurrukan gaggawa jiya Jumma'a a zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York. Ya kara da cewa, "Muddun ba a aiwatar da takunkuman ba, yiwuwar Koriya Ta Arewa ta kawo karshen shirinta na nukiliya za ta dusashe."
Pompea ya yi tozali da takwaran aikinsa na Koriya Ta Ludu Kang Kyung-Wha da kuma Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutterres. Ya kuma yi bayani ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasar Japan game da ziyarar da ya kai Koriya Ta Arewa a farkon wannan watan, lokacin da ya samu rakiyar Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley.
Facebook Forum