Yawan cin zarafin Larabawa da aka yi tsakanin 2015 da 2016 ya ribanya adadin da hukumar bincike ta FBI ta bayyana, wanda hakan ke nuni da irin raunin da ke tattare da kididdigar hukuma, a daidai lokacin da ake samun karuwar laifukan nuna tsana a kasar, a cewar wani cikakken rahoto na cibiyar Larabawa Amurkawa da ke Washington.
Bayan nazarin bayanai daga hukumomin tsaron jahohi, cibiyar ta yi kiyasin cewa an fuskanci take-taken tsanar Larabawa a Amurka har sau 79 a shekarar 2015, a maimakon guda 40 da hukumar FBI ta bayyana; da kuma sau 88 a 2016 a maimakon 58 da aka bayyana a rahoton kumar ta FBI.
Daga cikin manyan al'amura hudu da rahoton cibiyar ya yi kwatance da su, akwai kashe wasu matasa Larabawa uku da aka yi daura da Jami'ar North Carolina da ke Chapel Hill a 2015.
Facebook Forum