Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tace Ba Za Ta Yarda Rasha Ta Yiwa Jami'anta Tambayoyi Ba


Shugaba Trump
Shugaba Trump

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce Amurka ba za ta tura wani dan Amurka zuwa kasar Rasha domin a yi masa tambayoyi a kan tuhumar hada hadar fidda kudade ta barauniyar hanya.

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya bukaci masu binciken Amurka su je birnin Moscow su yiwa jami’an birnin tambayoyi a kan batun katsalandar zaben Amurka na 2016 da ake zargin Rasha da aikatawa, ciki har da tsohon jakadar Amurka a can Rasha din, kana ita kuma Rasha ta yiwa wasu jami’an Amurka tambayoyi.

Shugaban Amurka Donald Trump ya kira bukatar Putin a wurin taron kolin Amurka da Rasha a Helsinki bukata mai muhimmanci. Amma a hira da wannan gidan radiyo ta Muryar Amurka ta yi da Pompeo jiya Alhamis, ya yi fatali da wannan batu cewa Amurka ta bada yayanta Rasha ta yi musu tambayoyi.

Amurka ta tabbatar da laifi a kan wasu jami’an Rasha 12 na aikata kutse a komputocin kwamitin yakin neman zaben jami’iyar Democrat. Rasha ta bukaci rukunin masu binciken Amurka su yiwa wadannan jami’an tambayoyi kana daga bisani ita kuma Rasha ta yiwa jami’an Amurka 11 tambayoyi, ciki har da tsohon jakadarta Micheal McFaul.

Wannan batu na baiwa gwamnatin wata kasa damar yiwa jami’in diplomasiyar Amurka tambayoyi ya tsotsa ran wasu yan Republican a majalisun kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG