Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mutane Sun Nutse A Cikin Ruwa Yayin Da Suke Tserewa Harin ‘Yan Bindiga


Ana Ci Gaba Da Gano Gawarwakin Wadanda Suka Raso A Hatsarin Jirgin Ruwa A Zamafara
Ana Ci Gaba Da Gano Gawarwakin Wadanda Suka Raso A Hatsarin Jirgin Ruwa A Zamafara

Wasu mata da kananan yara da dama ne suka nutse a ruwa a lokacin da suke kokarin tserewa wani harin yan bindiga dauke da makamai a yankin arewacin Najeriya mai fama da rikici, kamar yadda mazauna yankin da wani jami’in gwamnati suka bayyana a jiya Alhamis.

Wadanda lamarin ya rutsa da su sun mutu ne a lokacin da kwale-kwalen su ya kife a lokacin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai musu hari na tsawon sa’o’i a daren Laraba a yankin Birnin Waje da ke jihar Zamfara, in ji wani mazaunin garin Ibrahim Zauma.

Ana Ci Gaba Da Gano Gawarwakin Wadanda Suka Raso A Hatsarin Jirgin Ruwa a Zamfara
Ana Ci Gaba Da Gano Gawarwakin Wadanda Suka Raso A Hatsarin Jirgin Ruwa a Zamfara

“Al’amarin ya yi muni saboda yawancin mutanen sun gudu daga gidajensu. Gawarwakin da aka gano kawo yanzu dai sun kai 13,” in ji Zauma.

Ba a dai bayyana ko nawa ne suka nutse ba, amma da dama da suka tsere daga gidajensu ba su koma yankin ba, lamarin da mazauna yankin suka ce ya kasance cikin rudani fiye da sa'o'i 24 bayan tashin hankalin.

Mutanen Da Suka Rasa Rayukansu A Hadarin kwale-kwale A Jihar Zamfara
Mutanen Da Suka Rasa Rayukansu A Hadarin kwale-kwale A Jihar Zamfara

Mai magana da yawun gwamnatin Zamfara, Ibrahim Bello, ya tabbatar da faruwar hatsarin, yana mai cewa “ba a san adadinsu ba, yawancin mata da kananan yara ne suka nutse a ruwa” yayin da suke neman tserewa a cikin kwale-kwale guda biyu.

Sai dai bai bayyana ko an kama yan bindigan ba.

Harin dai na daya daga cikin hare-hare na baya-bayan nan a jerin tashe-tashen hankula da kungiyoyi masu dauke da makamai suka kai wa al'ummomin yankunan arewa maso yammacin Najeriya da tsakiyar Najeriya.

Hukumomin kasar sun dade suna dora alhakin kai hare-haren kan gungun mafi yawan matasa makiyaya ‘yan kabilar Fulani da rikicin Najeriya ya rutsa da su tsakanin al’umma da makiyaya kan karancin ruwa da filaye.

Rikicin da ya janyo asarar rayuka tsakanin al’ummar yankin da makiyaya ya sha kan matakan da gwamnati ta dauka na kwantar da tarzoma, ko da yake a baya-bayan nan jami’an tsaro sun sanar da kama wasu da kwace makamai.

‘Yan bindigan a yawancin al’ummomin da abin ya shafa sukan fi karfin Jami’an tsaron Najeriya yayin da hukumomi kuma ke ci gaba da yakar tada kayar bayan da ‘yan tawaye masu kaifin kishin Islama suka kaddamar a yankin arewa maso gabas na tsawon shekaru goma.

~ AP

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG